Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga za ka yaƙa ba Nnamdi Kanu ba – Dangiwa Umar ga Buhari.

Published

on

Tsohon gwamnan mulkin soji na jihar Kaduna kanal Dangiwa Umar mai ritaya, ya caccaki jam’iyar APC da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sakamakon mai da hankali da su ka yi wajen kama jagoran masu fafutukar ƙafa ƴan tacciyar ƙasar Biafra Nnamdi Kanu maimakon mai da hankali kan yaki da taɓarbarewar tsaro.

 

Kanal Dangiwa Umar mai ritaya ya ce abin haushine kuma abin takaici maimakon gwamnatin shugaba Buhari ta mai da hankali wajen yadda za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan amma sai ta juya aƙalarta kan neman kama Nnamdi Kanu ruwa a jallo.

 

Tsohon gwamnan mulkin sojin na jihar Kaduna ya ce abin haushin shine yadda gwamnati da jam’iyyar APC suke ta zuzuta batun kama Nnamdi Kano bayan a gefe guda ga yan ta’adda na ci gaba da cin karansu ba babbaka.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!