Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda Dilolin magunguna a Kano suka yi zanga-zangar lumana

Published

on

Ƴan kasuwar magani da ke jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan titin gidan gwamnatin Kano kan yadda suka ce an tilasta musu tashi daga kasuwar su da kuma kulle musu shaguna.

Shugaban Ƴan ƙungiyar ƴan maganin Alhaji Musbahu Yahaya ne ya jagorancin zanga-zangar lumana inda suke kira ga gwamnati da tayi duba da irin halin matsi da suke ciki a wannan lokaci wajen kawo musu daukin gaggawa.

Alhaji Musbahu Yahaya ya ce dalilin su na ƙin amincewa da komawa kasuwar Ɗangoro shi ne, la’akarin da yadda kasuwar da Ɗangoro ta kasance mallakin su mutane ba ta gwamnati ba kuma adadin shagunan da suke wajen bazasu ishi ƴan kasuwar ba, da a ƙalla sun kai sama da 3000 su da suke gudanar da kasuwancin na magani kuma ita wannan kasuwar shagunan cikin ta basu huce 600 ba.

“A dan haka idan gwamnati zata shiga lamarin ya kasance kasuwar a hannun gwamnati take su a shirye suke su koma amma a yanzu kuɗin da aka sanya a matsayin kuɗin haya yayi yawa la’akari da yadda akace koya sai ya biya miliyan 3 kudin haya maimakon Dubu 300 zuwa Dubu 500 da suke biya A cewar Shugaban”

Da yake jawabi Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya sami wakilcin shugaban ma’aikatar fadar gwamnati Alhaji Shehu Wada Sagagi ya ce gwamnati zata bibiyi yadda aka rufe shagunan ƴan kasuwar maganin dake jihar domin samarwa da ƴan kasuwar sassauci kan yadda a yanzu shuka shafe kwanaki ba tare da sun gudanar da kasuwancin su ba.

Sagagi ya ƙara da cewa zasu kira shugabannin hukumomin da suke da alhakin rufe shagunan nasu domin tattaunawa da su kan lamarin.

Gwamnatin kano ta kira shugaban ƙungiyar domin tattaunawar sirri domin samar da mafita kan halin da suke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!