Connect with us

Labarai

Ƴan sanda sun ceto mutane daga hannun ƴan bindiga a Zamfara

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kuɓutar da wasu mutane 8 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴansandan jihar SP. Shehu Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, a ranar 25 ga watan Agustan da muke ciki ne, ƴan bindiga suka sace mutanen 8 a garin Kangon Sabuwa da ke ƙaramar hukumar Bungudu.

SP. Shehu Mohammed ya ƙara da cewa, an kuɓutar da mutanen cikin ƙoshin lafiya, har ma an miƙa su ga iyalansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!