Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun kama Ɗan Sarauniya a Abuja

Published

on

Ƴan sanda sun kama tsohon kwamishina aiyuka da raya birane na jihar Kano Engr Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya jim ƙaɗan bayan kammala tattaunawarsa da gidan talabijin na Trust TV dake utako a birnin tarayya Abuja, a daren jiya Alhamis.

Wata majiya da ta ga yadda lamarin ya faru tace, da fari Ɗan Sarauniya ne ya samu wani mummunan haɗari a titin Ngozi Okonjo Iwela, har ta kai ya daki fitilar kan titi da motarsa ƙirar Honda har jakar iskar motar fita.

Dai dai lokacin da yake duba motar tasa ne ƴan sandan suka cafkeshi, wanda har kawo wannan lokaci basu bayyana dalilin kama shin ba, sai dailauyan sa Barista Garzali Datti Ahmad ya Shaidawa BBC cewa suna zargin Gwamnatin Kano ce ta sa a kama shi.

A ranar 17 ga watan Janairun 2022 ne ƴan sanda a Kano suka gayyaci Mu’azun domin amsa wasu tambayoyi, sai dai bai sami zuwa ba, inda ya tura lauyansa ya wakilceshi

Tuni dai Ɗan sarauniya ya koma tsagin Malam Shekarau bayan saɓanin jam’iyya da suka samu, Mu’azu Magaji dai yayi sunan wajen sukar lamirin Gwamna Ganduje a kafafen sada zumunta bayan da aka sauke shi daga muƙaminsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!