Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun kama masu sayowa ƴan bindiga man fetur a Katsina

Published

on

Rundunar ƴn sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane 5 da ta ke zargin suna kai wa ƴan bindiga man fetur.

Kazalika rundunar ta zargi cewa su ma suna da alaƙa da yin garkuwa da mutane.

Mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa.

Ya ce, a ranar 18 ga watan Satumba rundunar ta samu nasarar cafke guda daga ciki a Maraɗi ta jamhuriyar Niger, sai kuma wani a Magamar Jibia dukkanin su ɗauke da man fetur akan babura.

Kazalika an kama ɗayan a ƙauyen Daddara da ke Jibia shi ma zai kai wa ƴan bindigar Mai a cikin motar sa, sai wani a ƙauyen Anguwan Nakaba a ƙaramar hukumar Sabuwa.

Isah ya kuma ce, rundunar ta kama wani ɗan shekara 30 a Sabon Garin MotsoMotso a ƙauyen Zandam da ke ƙaramar hukumar Jibia da laifin kai wa ƴan bindiga bayanai da kuma sayo musu burodi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!