Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan Soshiyal Midiyan APC masu tallan Tinubu a Arewa sun tafi yajin aiki

Published

on

Haɗakar ƙungiyoyin ƴan Arewa masu amfani da kafafen sada zumunta wajen tallata Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC Bola Ahmad Tinubu sun tafi yajin aikin sai baba ta gani.

Hakan na cikin wata sanarwa da suka aike wa Freedom Radio, mai ɗauke da sa hannun Shugaban Haɗakar Ƙungiyoyin Malam Rabi’u Biyora da Sakatarensa Khalid Ibrahim Angale.

Sanarwar ta nemi dukkan ƴan soshiyal midiya daga ƙungiyoyi daban na jihohin Arewa 19 da birnin tarayya Abuja kan su dakatar da duk wani motsi na tallata tafiyar Bola Tinubu da Kashim Shetima.

Haɗakar ƙungiyoyin sun kuma nemi mambobinsu da su yi haƙuri su saurari saƙo na gaba.

Idan zaku iya tunawa tun bayan babban taron yaƙin neman zaɓen a APC a birnin Jos na jihar Filato aka samu sabon rikici a tafiyar ƴan Social Media.

Inda suka zargi ba a basu kulawa ba, ana kuma nuna musu fifiko tsakaninsu da ƴan Film.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!