Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kowane Gauta

Ɓaraka ta kunno kai a tsakanin sojojin bakan Ganduje

Published

on

A makon da ya gabata ne rikici ya kunno kai a tsakanin sojojin bakan dake kare muradun gwamnatin Kano a kafafan yada labarai bayan da maitaimakawa gwamnan Kano kan kafofin yada labarai Shehu Isa Direba ya kafa kwamitocin ‘yan baka a ma’aikatun gwamnatin Kano.

Sai dai wannan yunkurin nasa ya bar baya da kura, inda wasu ke goyan bayan sa, a gefe guda wasu kuma ke ganin baiken sa.

A kan haka ne Aminu Black Gwale na jam’iyyar APC ya soki yunkurin da Shehu Isa Direba ya yi, yana mai cewa akwai manufar yin hakan domin shirin sa na tsayawa takara.

Aminu Black Gwale ya bayyana haka ne ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom Radio yana mai cewa Shehu Isa direba dan aike ne na Usman Alhaji Usman wato sakataren gwamnatin Kano, domin su rusa tafiyar kwamshinan yada labarai na Kano Muhammad Garba a don haka Aminu Black ya ce dole su kare Muhibbar Kwamishinan

Ya ce, wannan ya nuna cewa akwai abin da suke shiryawa ta karkashin kasa kuma sun gano su, ba zasu zuba ido hakan ta ci gaba da faruwa ba saboda suna da wata bukata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!