Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kowane Gauta

Rikicin siyasa na kara ruruwa a kasuwar Kantin Kwari

Published

on

Bilal Musa Bakin Ruwa jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Kima ta kasuwar kantin kwari ya kalubalanci gwamnatin jihar Kano kan gaza gudanar da zabe a kasuwar.

Yana mai cewar rashin gudanar da zabe a Kasuwar ta Kantin Kwari ya sanya ake tafka kura-kurai.

Bilal Musa ya shaida hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na gidan Radio Freedom.

Yana mai cewa shekara da shekaru gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kasa gudanar da zabe a kasuwar wanda yasa yanzu kowane kamfani ke yin abinda ya ga dama a kasuwar.

Bilal ya kara da cewa babu wata rawa da shugabancin ruko na kasuwar ke gudanarwa a yanzu haka , domin kawo gyara musamman akan kamfanoni dake yin badai-dai-ba ko cin-karen-su-ba-babbaka a kasuwar wanda ya sabawa doka amma sun kasa takubaka komai akai.

Yace mafita kawai gwamna Ganduje ya fitar da tsarin gudanar da zabe a kasuwar domin hakan shine kadai zai fi a’ala a kasuwar baki daya.

Su dai ‘yan kasuwa da dama na kukan rashin ciniki a halin yanzu kasancewar  al’umma na cikin wani hali tun bayan da kasar nan ta shiga cikin jerin kasashen da fuskanci annubar Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!