Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ɗaliban jami’ar tarayya a Gusau sun gudanar da zanga-zangar lumana

Published

on

Ɗaliban jami’ar tarayya da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna damuwa kan garkuwar da ƴan ta’adda suka yi da ƴan uwansu ɗalibai.

Ɗaliban waɗanda suka yi zagaye a birnin Gusau, sun kuma rufe babbar hanyar da ta tashi daga Gusau zuwa garin Funtua na jihar Katsina.

Rahotonni sun ce, a daren Jumu’ar da ta gabata ne ƴan bindiga suka yi garkuwa da ɗaliban a yankin Damba da ke dab da shiga birnin Gusau.

Jihar ta Zamfara dai na cikin jihohin da ke fama da hare-haren ƴan ta’adda masu yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!