Connect with us

Tsaro

Ɗalibar BUK da ƴan bindiga suka sace ta shaƙi iskar ƴanci

Published

on

Ɗalibar jami’ar Bayero anan Kano da ƴan bindiga suka sace ta shaƙi iskar ƴanci.

Ɗalibar mai suna Sakina Bello tana aji na 3 a jami’ar, ta shaƙi iskar ƴancin da yammacin ranar Alhamis.

Tun da fari ƴan bindigar sun sace Sakina ne a hanyar Janbulo zuwa Rijiyar Zaki bayan fitowar ta daga gida.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kuɓutar ɗalibar ta bakin mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a zantawar sa da jaridar Solacebace.

Kiyawa ya ce, an gano Sakina a unguwar Sabon Gari bayan da ta kira iyayen ta a waya tana shaida musu yadda ta kuɓuta daga inda aka ɓoye ta.

DSP Kiyawa ya ce, babu wani kuɗin fansa da aka biya gabanin sakin nata, kuma tuni an damƙata ga iyayen ta, kuma za a ci gaba da bincike don gano masu hannu a lamarin.

Idan za a iya tunawa ƴan bindigar sun buƙaci a biya kuɗin fansa da ya kai Naira miliyan 100bkafin su sake ta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!