Connect with us

Labarai

Ɗan Sarauniya ya goyi bayan Baffa kan ƴan adaidaita sahu

Published

on

Tsohon Kwamishinan ayyuka na Gwamnatin Kano Engr. Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya ya goyi bayan hukumar KAROTA kan tilasta wa masu adaidaita biyan kuɗin haraji.

A cikin wani saƙon murya da ya aike wa Freedom Radio, Ɗan Sarauniya ya ce, abin da KAROTA ta yi daidai ne, kuma abu ne da ya dace a yi tun a baya.

Ya ce, bai ga abin ta da jijiyar wuya ga ƴan adaidaita ba, don kawai an ce su bayar da Naira ɗari-ɗari kullum.

Ya ƙara da cewa, ƴan adaidaita na amfani da tituna da tsaron jiha da lantarki na Gwamnati saboda haka babu dalilin da za su ƙi biyan wannan haraji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!