ilimi
Ƙalubale 10 da bangaren ilimi a Kano ke fuskanta
Mai sharhi kan al’amuran ilimi kuma malami a tsangayar ili a jami’ar Bayero da ke nan Kano ya bayyana tsarin ilimi kyauta kuma dole da gwamnatin Kano ta fito da shi a matsayin abinda bai tasiri ba.
Dakta Idris Salisu Rogo ne ya bayyana hakan ta cikin shirin “Duniyar mu a yau” na nan Freedom Radio.
Rago ya ce “tun bayan ayyana tsarin ilimi kyauta shekaru biyu da suka gabata, gaba ɗaya harkar ilimi ta sake lalacewa musamman a matakin Firamare”.
Dakta Rogo ya lisaffa ƙalubale 10 da bangaren ilimi ke fuskanta a jihar Kano kamar haka:
1- Har yanzu gwamnati ba ta san walwalar malaman makaran ta ba.
2- Rashin kayan aiki ga malamai.
3- Rashin kyakyawan muhallin karatu ga ɗalibai da malamai.
4- Rashin tura malamai karo karatu don ƙwarewa.
5- 3 Rashin ɗaga likkafar malamai zuwa mataki na gaba wato Promotion.
6- Rashin kyakyawan albashi.
7- Ɗaukar malamai marasa kwarewa a fannin.
8- Rashin samar da wadatattun malamai a makarantu.
9- Rushe tsarin Zonel Office wanda su ke bibiyar makarantu.
10- Rashin samar da shugabanci mai kyau a makarantu.
Rogo ya ce, matukar aka ci gaba da tsarin bada ilimi kyauta koma dole to kuwa harkokin ilimi zai shiga cikin mawuyacin hali.
You must be logged in to post a comment Login