Labarai
Ilimi kyauta kuma dole ya haifar da cinkoson dalobai a Kano – SUBEB
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2022/12/FB_IMG_1670848038801.jpg)
Hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano SUBEB ta ce, shirin bada ilimi kyauta kuma dole ya haifar da cinkoson dalibai a makarantun Firamare a Kano.
Shugaban hukumar Dakta Danlami Hayyo ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan kaluablen da harkokin ilimi ke fuskanta a yanzu.
Dakta Danlami Hayyo ya kuma ce, batun korafin da wasu malamai suke yi na rashin yi musu karin albashi yana da alaka da rashin basu takardar karin girma a rubuce.
Da yake batu kan shagunan da ake ginawa a jikin makarantu’ Danlami Hayyo ya ce “Da zan samu ikon zama gwamna na yini daya a Kano da duk sai na rushe shagunan da aka gina a jikin makarantun”.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ilimin Firamare ke ci gaba da fuskantar kalubale.
You must be logged in to post a comment Login