Labarai
Ƙananan hukumomi na fuskantar karancin kudi -Ado Tambai Kwa

Karamar hukumar Dawakin Tofa ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta samar musu da ayyukan ci gaba kamar yadda take yi a jihar nan.
Shugaban karamar hukumar Ado Tambai Kwa, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da freedom radio, inda yace babban kalubale da kanan hukumomi a yanzu suke fuskanta shi ne na rashin kudi a hannun su.
Ado Tambai Kwa yace da ana bawa ƙanan hukumomi kudi a hannu na gudanarwa da sunyi ayyukan cigaba fiye da wanda suke yi.
You must be logged in to post a comment Login