Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Zan fara koyar da darasin Physics a makarantun Dawakin Tofa- Shugaban karamar hukuma

Published

on

Ado Tambai Kwai ,Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa

Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa yace daga zangon karatu mai kamawa zai fara koyar wa a makarantun yankin shi da ‘yan majalisar sa .

Ado Tambai Kwa ya fadi hakan ne lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyon Freedom .

Da aka tambayi Ado Tambai Kwa ko me zai koyar a zangon karatu mai kamawa yace zai iya koyar da darasin Physics tunda shi injiniya ne har ma da darasin lissafi .

Yace tun  rantsar da shi a matsayin shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa ya bayar da karfi wajen habaka ilimi a yankin.

Ado Tambai Kwa yace akwai yara da dama da ba sa iya zuwa makaranta sakamakon rashin abun hawa da kuma rashin karfi  na iyayen su.

Yace hakan ce ta saka ya sayi motci guda uku masu mazauni guda hamsin domin kaiwa da dawo da yara makaranta.

A bangaren kudaden shiga kuwa yace sanda ya karbi ragamar shugabancin karamar hukumar ta Dawakin Tofa Naira dubu dari biyu da hamsin kacal suke samu amma da ya like guraran da suke zurara a yanzu suna samun kimanin Naira miliyan uku ko fiye a duk wata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!