Kasuwanci
Ƙaratowar Azumi: Muhyi ya gargaɗi ƴan kasuwar Dawanau kan ƙara farashi
Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta gargaɗi ƴan kasuwar Dawanau, game da ƙara farashin kayayyaki a daidai lokacin da watan azumi ke ƙaratowa.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya jagoranci tawagar hukumar zuwa kasuwar don tattaunawa a ranar Laraba.
Muhyi ya ce, ba sa fatan a sake maimaita abin da ya faru a bara, na ƙara farashin kayayyaki saboda haka suke gargaɗar ƴan kasuwar.
Da yake mayar da jawabi shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar ta Dawanau Alhaji Saleh Ahmad Ƙwa ya ce, za su yi iya ƙoƙarin su wajen ganin ba a samu ƙarin farashin kayayyaki ba.
Ya ce, abin da ya dace shi ne ƴan kasuwa su sassauta farashi ko don su samu tagomashi daga Ubangiji.
Alhaji Saleh Ƙwa ya ce, ba su da wani shiri na ɓoye kayayyaki ko ƙara farashi, kuma ba za su yi sakaci hakan ta faru ba.
Wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewa, Muhyi Rimin Gado na tare da rakiyar jami’an tsaro da wakilan ƙungiyoyin kasuwa inda suka ci gaba da zagayawa zuwa sauran kasuwanni.
You must be logged in to post a comment Login