Ƙetare
Ƙasashe 17 sun nemi ƙungiyar Hamas ta zubar da makamanta

Ƙasashen Larabawa da dama sun nemi ƙungiyar Hamas ta zubar da makamanta kuma ta haƙura da mulkin Zirin Gaza domin kawo ƙarshen yaƙin da Isra’ila ke yi a Zirin.
Ƙasashe 17 ne suka bukaci haka ciki har da Tarayyar Turai inda ƙungiyar hadin kan Larabawa suka fitar da wata sanarwa mai shafi bakwai a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kiran a farfaɗo da batun kafa ƙasa biyu, wato ta Falasɗinu da kuma Isra’ila.
“A yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin nan, dole ne Hamas ta kawo ƙarshen ikonta a Gaza kuma ta miƙa makamai ga Hukumar Falasɗinawa…kamar yadda manufar kafa ƙasar Falasɗinu ta tanada,” a cewar sanarwar.
A ranar Litinin ne hukumar ta Falasɗinawa wato Palestinian Authority ta nemi Hamas da Isra’ila duka su fice daga Gaza domin ba ta damar karɓe iko da zirin.
Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya jawo ɓarkewar yaƙin.
You must be logged in to post a comment Login