Labarai
Ƙungiyar ƴan Robobi ta ƙaddamar da aikin rage cunkoson a kasuwar Wambai

Ƙungiyar masu sayar da Robobi ta jihar Kano, ta ja kunnen mambobinta da kuma masu sayar da kayan Gwanjo a kan titin Masallacin Idi da su guji kasa kaya a kan titi ko kuma ta ɗauki matakin ba sani ba sabo a kansu.
Shugaban Riƙo na Ƙungiyar Alhaji Sadi Mai gida Warure, ne ya yi wannan gargaɗi yayin gudanar da aikin tsaftace titin ta hanyar matsar da masu kasa Kaya a kan titi domin samun sauƙin masu wucewa.
Ya ce, suna da matakan da suke dauka kan duk wanda suka samu da laifin karya doka ta hanyar haddasa cinkoso.
Shi kuwa Alhaji Adamu Gyaranya jagoran gwagwarmaya ƙungiyar a ƙungiyar ƴan robobi ta jihar Kano, ya yaba da yadda shugabannin ƙungiyar suka gudanar da aikin.
Shi kuwa Alhaji Ibrahim Maitama, daya daga cikin wadanda aka kafa shugabancin hadin gwiwa da su a kasuwar, ya bayyana jin dadinsa bisa gudanar da aikin ya na mai cewa, za su ci gaba da sanya ido wajen ganin cewa kasuwar ta ci gaba da kasancewa bisa tsari mai kyau.
You must be logged in to post a comment Login