Labarai
Ƙungiyar Lauyoyin Jigawa ta yi sabbin shugabanni

Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Jigawa ta gudanar zaben sabin shugabannin cin kungiyar na jiha inda aka fafata tsakanin mutane uku dake neman shugabancin ta.
Wadanda aka zaba din sun hada da Barista Garba Hamza Umar, a matsayin sabon shugaba sai Barista Saminu Sanusi mataimaki da Barista Kabiru Adamu a matsayin Sakandiren kungiyar.
Sauran su ne: Barista Muhammad Ahmad Auwal ma’aji da Muhammad Iliyasu Sa’idu mataimakin sakatare da kuma Barista Adamu Baba Doko Umar a matsayin sakataran yada labaran kungiyar da Ibrahim Ahmad mai kula ka’idojin da dai sauran su.
Barista Garba Hamza, ya samu nasara a kan abokan karawarsa guda biyu da kuri’u 60 ya sai na biyu guda 35 da na uku Umar Shehu Abubakar mai kuri’a 8.
You must be logged in to post a comment Login