Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA ta rabe gida biyu –Barista Nuhu

Published

on

Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA ta rabe gida biyu sakamakon bullar wata sabuwar kungiyar da ta kira kanta da suna sabuwar kungiyar lauyoyi ta kasa NNBA wato New Nigerian Bar Association.

Lauyoyin da suka balle daga uwar kungiyar ta NBA dai tare da kafa kungiyar ta NNBA sun ce sun dau wannan mataki ne domin nuna adawarsu da cire sunan gwamnan jihar Jigawa Malam Nasir El-rufai cikin wadanda za su gabatar da mukala a yayin taron shekara-shekara da kungiyar ta gudanar.

A cikin wata sanarwa da sabuwar kungiyar ta fitar a jiya Talata, ta ce, sabuwar kungiyar ta kunshi lauyoyi ne wadanda suka fito daga yankin arewacin kasar nan, kuma nan gaba kadan ba da dadewa ba za a kaddamar da ita.

Sanarwar wadda Barista Nuhu Ibrahim da Barista Abdulbasit Suleiman suka sanyawa hannu ta ce, kungiyar ba za ta lamunci irin cin fuskar da ake yiwa arewacin kasar nan.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!