Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar AA Zaura

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun sace mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Abdussalam Abdulkarim Zaura.

Al’amarin ya faru ne a daren jiya Lahadi a gidanta da ke garin Zaura na mazaɓar Rangaza a ƙaramar hukumar Ungoggo.

Mai magana da yawun ƴan sandan Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar al’amarin.

Ya ce “Mun tura jami’anmu sun ci gaba da bincike kan lamarin, don a gano maɓoyarsu”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!