Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sponsored: Shekaru Bakwan Ganduje na inganta rayuwa da ci gaban Kanawa

Published

on

Daga Aminu Dahiru Ahmad
Harama tayi nisa dan zabar sabbin shuwagabannin da za su maye gurin gwamnoni da shugaban kasar dake kan karagar mulkin a shekarar 2023.
A Jiharmu ta Kano mai dimbin tarihi da albarka tuni Mataimakin Gwamna Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe zaben fidda gwani na dantakarar gwamna a Jam’iyyarmu ta APC mai alamar tsintsiya. Dama can Nasiru yusuf Gawuna shi ne wanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zaba dan ya gajeshi.
Tsohon komishinan kananan hukumomi, Alhaji Murtrala Sule Garo shi ne wanda zai mara wa mataimakin gwamnan kuma dan takarar gwamna baya a zaben sheka mai zuwa.
Wannan da wasu dalilai su ka sa zamuyi waiwaye kan ayyukan more rayuwa da gwamnatin Dakta Abdullahi Ganduje ta aiwatar, harma da dokoki da tsare-tsare da ta bijirowa da jihar dan bunksa rayuwar al’umma.
Da farko dai an zabi Gwamna Ganduje a matsayin gwamna karo na farko a shekarar 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Gwamnan ba dami ya tsinta a kale ba, gogaggen ma’aikacin gwamnati ne kuma dan siyasa ne tun daga tushe har takai ga ya yi mataimakin gwamna har sau biyu. Wannan ta bashi damar fahimtar matsalolin da kalubalen da jihar ke fuskanta.
A fili yake cewar a tarihi na kusakusannan ba bu wani gwamna da ya narka aiki a wannan jiha a zahiri ba labari ba kamar mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Makaranci ka biyoni a hankali a yayinda zan zayyano ayyukan more rayuwa da kuma kuma dokoki da gwamnan ya kawo ga wannan jiha a cikin shekaru bakwai da wasu watanni da su ka gabata. Wadanda suka hada da bunkasa ilimi da lafiya da tattalin arziki da bunkasa sufuri da noma da kiwo da samar da aikinyi da sauran ayyukan raya kasa da cigaban al’umma.
Ilimi
Bayan dogon nazari da tuntuba, a shekarar 2019 mai girma gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar bada ilimi kyauta kuma dole tun daga matakin firamare har zuwa sakandire a jihar.
Sanya hannu kan wannan doka ya wajabtawa iyaye sanya ‘ya’yansu a makarantar boko musamman wadanda su ka kai munzalin fara karatu.
Wannan saban tsari da gwamnan ya bijiro da shi dan inganta ilimi da rayuwar al’umma a jihar ba karamin al’amari ba ne.
Akwai bukatar kudi da aiki da lura da kuma jajircewa domin canja akalar ilimi har a cimma gaci.
Kafin fitar da wannan sabuwar doka Jihar Kano ce ke da adadi mafi tsoka na yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya wanda ya kai kimanin miliyan guda da rabi.
Wannan saban tsari ya bawa gwamnatin dama wajen tursasa iyaye su saka ‘ya’yansu a makaranta. A yanzu haka makarantu 1018 ne ke lakume kimanin biliyan hudu da digo biyu N4.2 billion duk shekara kamar yanda gwamnatin ta tanada dan inganta ilimi a hijar.
Ba anan gwamnatin ta tsaya kawai ba. Gwamnatin ta durfafi makarantu allo dan ingantasu su su dace da zamani.
Wannan ya hada da kikirar hukumar da ke lura da makarantun allo da na Islamiyya a jihar.
Gwamnatin ta samar da malamai da ke koyar da Ingilishi da lissafi a irin wadannan makarantu, sannan ta gina manyan makarantun kwana na almajirai a kowace shiya ta jihar da kuma samar da alawus ga alarammomi.
Duk wannan na yiwuwa ne a daidai lokacin da gwamna Ganduje yake da dawainiya wajen biyan Biliyoyin basukan karatun daliban dake kasashen waje wanda ya gada daga gwamnatocin da suka shude
Sabbin Masarautu
Haka zalika gwamnatin Jihar Kano karskashin mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro sabbin masarautu masu daraja ta daya a jihar har guda hudu a Bichi da Gaya, da Rano da Karaye.
Wannan ya biyon bayan kudirin gwamnatin na kirkirar birane a jihar musamman a cikin sabbin masarautun, da kuma fadada gwamnati. Dama can al’ummar wadannan yankuna nata kiraye-kiraye da gwamnatin ta daga darajar masauratunsu har Allah ya kawo lokacin da Gwamnan ya cika musu burin su.
Tun bayan kirkiro masarautun gwamnatin ta dukufa wajen gudanar da ayyukan more rayuwa a wadannan yankuna. Wannan ya hada da gina tituna da daga darajar asibitoci da da gina manyan makarantu da inganta harkar tsaro da samar da ayyukanyi da kuma matso da gwamnati kusa da al’umma.
Mutannan da ke yankunan tuni su ka bada shedar cewar sunfi kusanci da gwamnati a yanzu fiye da shekarun baya.
Lafiya
A lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dawo a karo na biyu a shekara ta 2019 ya tabbatar da cewar gwamnatinsa za ta cigaba da baiwa bangarorin ilimi da lafiya fifiko sama da komai kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta shaida cewa duk kasar dake son cigaba dole ne sai ta fifita wadannan bangarori guda biyu.
Ayyuka da a ka samu a wannan bangaren na lafiya sun hada gina asibitoci a dukkannin sabbin masarautin jihar hudu wadanda za su ci gadaje dari hudu domin bunkasa harkar lafiya a jihar baki daya.
Haka zalika gwamnatin ta daga darajar asibitoci a dukkannin kananan hukumomin da ke jihar guda arba’in da hudu.
Cutar daji wato kansa na daya daga cikin cututtukan dake addabar al’ummar Nijeriya. Duk shekara cutar na sanadiyyar mutuwar mutane a kasar.
A karkashin tsarinta na lafiya jari, daga lokaci zuwa lokaci gwamnatin na bawa marasa lafiya tallafi na musamman. Wannnan ya hada kayan haihuwa ga masu juna biyu da kuma magani da aiki ga masu fama ciwan ido. Dubban al’ummar kanawa sun amfana da wannan tsari.
Ginin Cibiyar Yaki da Cutar Daji
A wani bangaren kuma Jihar Kano na daya daga cikin jihohi dake fama da wannan cuta. Hakan yasa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gina cibiyar yaki da wannan cuta wanda masu kudi da talakawan wannan kasa duk za su zo Jihar Kano dan samun waraka. Yanzu haka saura kiris a kammala wannan katabariyar cibiya da ke Asibitin Muhammadu Buhari da ke Giginyu.
Duk wannan na zuwa ne bayan da Gwamnan ya kammala gina sabbi da kuma inganta manyan asibitocicin jihar da samar musu da manyan na’urori na zamani musamman Asibitin yara na Sheikh Isyaka Rabi’u dake Titin Gidan zoo da kuma Asibitin Muhammadu Buhari dake Unguwar Giginyu wadanda ya gada daga Gwantocin da suka shude kuma ya kammala su.
Samar Da Ayyukanyi
Bayan tallafi da gwamnatin jihar Kano ke bawa matasa duk shekara tun daga 2015 izuwa yau, gwamnatin ta bijiro da wasu tsaruka dan inganta rayuwar matasa da mata a jihar.
Gwmanati ta aike da Daruruwan matasa zuwa kamfanin Peugeot da ke Jihar Kaduna dan su samu horaswa ta musamman akan gyaran mota a zamanance. Da yawa daga cikin wadannan matasa yanzu haka na sana’ar gyaran mota a sassa daban daban na jihar.
Haka zalika gwamnatin ta gina katafariyar cibiyar koyar da sana’o’i wato Dangote Skills Acquisition Centre wadda ke da guraban horaswa guda 22.
Duk wadannan ayyuka anyi su ne akan kudirin rage rashin aikinyi a jihar kano da yalwata tattalin arziki.
Binkasa sufuri
Jihar Kano babbar cibiyar kasuwanci ce ta Najeriaya harma ga wasu daga kasashen da ke yammacin Afirka. Dan haka idan ana bukatar inganta kasuwanci sai an bunkasa sufuri a jihar dan a kullum dubban mutane ne daga jihohin Najeriya daban daban da wasu kasashe dake makwabtaka da wannan kasa ke shigowa jihar dan yin kasuwanci.
Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje tai la’akari da hakan wajen gina manyan tituna da gadajen sama dana kasa domin rage cinkoson ababan hawa da inganta sufuri a jihar.
Akalla gwamnatin ta gina gadojin sama dana kasa guda shida wanda sun hada Dangi Interchange by Zoo Road Kano, Muhammadu Buhari Interchange dake Bypass, Kofar Mata/Kantin Kwari/Ibrahim Taiwo Flyover, Panshekara Madobi Underpass, Tijjani Hashim Kofar Ruwa Underpass, da Alhassan Dantata Flyover, wadda na daga cikin gadojin sama mafi tsayi a Afrika, da dai sauransu.
Noma da kiwo
Wannan makala ba za ta kammala ba sai an tabo fannin noma domin ita ce tushen arziki da Kuma kiwo.
Arewacin Najeriya na da tarihin noma. A Jihar Kano kananan hukumomi da yawa sun shahara a fannin noma.
Dan haka tun kafin gwamnatin tarayya ta maida hankali kan habaka tsarin noma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dukufa wajen habaka kamfanin taki na KASCO da noman Tumatir, Alkama da Shinkafa.
Yanzu haka saboda wannan tagomashi masana’antun shinkafa da manomanta sun zage dantse dan ganin Jihar ta kara daukan tuta a wannan bangaren kamar yadda tayi lokuta da dama. A yanzu haka Jihar Kano ita ce kan gaba wajen sarrafa shinkafa kamar yanda gwamnatin tarayya ta tabbatar.
A bagaren kiwo Kuma gwamnatin ta samarwa da makiyaya gurabe na zama wuri daya dan habaka kiwo. Gwamnatin ta raba irin ciyawa kyauta da Samar da kasuwanni na zamani dan inganta kasuwancin madarar Shanu ta hanyen yin allurar shanu kyauta.
Domin cigaban wadannan ayyuka na inganta rayuwa da cigaban al’umma ne Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayi duba na tskanaki wajen zakulo mataikin sa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon kwamishinan kananan hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo domin cigaba duba da kwarewa da gogewar su wajen gudanar da harkokin al’umma.
Ga wasu ayyukan a cikin hotuna:
Aminu Dahiru Shine mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a fannin hotuna.
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!