Labarai
Ƴan Fansho sama da dubu 32 ne suke bin gwamnati bashin Naira biliyan 20 – Sani Gabasawa
Hukumar fansho ta jihar Kano ta ce a yanzu ba ta iya biyan kuɗaden ƴan fansho yadda ya kamata sakamakon halin matsi da aka shiga.
Hukumar ta ce, halin da aka shiga ya samo asali daga yadda annobar corona ta shafi tattalin arziƙi.
Shugaban hukumar Alhaji Sani Dawaki Gabasawa ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen zaɓen sababbin shugabannin ƙungiyar a jihar Kano.
Sani Dawaki Gabasawa “Yace matsalar kuma na ƙara ta’azzara ne sakamakon yadda ake ƙara samun waɗanda suka yi ritaya ba kuma tare da an bai wa hukumar abinda ya kamata daga gwamnatin ba”.
“Rabon da hukumar mu ta biya kuɗin Fansho da ariya tun a watan Yunin shekarar 2016, wanda shi ma hakan ya faru ne sakamakon rashin cika umarni na doka da wasu hukumomin ke yi”.
Sani Dawaki ya kuma ce “Yan Fansho sama da dubu 32 a jihar Kano, da suke bin gwamnatin bashin sama da Naira Biliyan 20, sai dai yace sun zauna da gwamna tare da shawarwari guda 8 kan yadda za’a kawo karshen matsalar.
You must be logged in to post a comment Login