Labarai
Ƴan sanda sun bankaɗo wasu motoci da suke lodi ba bisa ƙa’ida a ba tashar Rijiyar Lemo
Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta kama motoci 11 bisa zargin yin lodi ba bisa ƙa’ida ba.
Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan kai sumame tashar da safiyar Alhamis ɗin nan.
Ya ce, sun samu ƙorafi a kan tashar Kurna da ke yankin Rijiyar Lemo anan Kano, kan zargin cewa suna lodin fasinja ba bisa ƙa’ida.
Kiyawa ya kuma ce, rundunar ta kama wani matashi da yayi barazana ga jami’an ƴan sanda lokacin da suke aikin binciken motocin da ake zargi a tashar.
Har ma ya ce, zuwa yanzu rundunar ƴan sanda sashin MTD karkashin jagorancin SP Magaji Musa Majiya, ta zauna da direbobin domin daukar matakin da ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login