Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar Yan sandan ta haramta amfani da Jiniya ba bisa ka’ida ba

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta haramta yin amfani da Jiniya a motoci ba bisa ka’ida ba, ciki har da jami’an rundunar wadanda ke amfani da jiniyar ba bisa ka’idah ba.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sandan Kano Muhammad Hussain Gumel, ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

Haka zalika SP Kiyawa, ya ce, rundunar ta kuma haramta rufe lambar motoci da wasu mutane ke yi, tare da bada umarnin kama duk wanda aka samu da laifin karya wannan doka.

 

Rahoton; Abdulkarim Muhammad Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!