Labarai
Ƴancin Kai: Buhari ya gindaya sharuɗa domin janye takunkumin da ya sanya wa Twitter
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin janye takunkumin da aka sanya wa kamfanin Twitter a kasar nan tun a watan Yunin da ya gabata.
Buhari ya bayar da umarnin ne, a wani bangaren na bikin cika shekaru 61 da samun yancin kai.
Shugaba Buhari ya ce kafin dauke takunkumin gaba daya, dole kamfanin su cika wasu ƙa’idojin da aka gindaya musu.
Ƙa’idojin sun haɗar da bai wa al’ummar ƙasar nan damar gudanar da kasuwanci a dandalin ba tare da tsangwama ba.
Ko da yake shugaban ya gamsu da irin muhimmancin da kafafen sadarwa na zamani ke da shi, amma ya ce abin takaicine yadda wasu ke amfani da su wajen raba kan al’umma.
“Kafafen sadarwa na zamani na da matukar muhimmanci, da suke bai wa miliyoyin al’ummar ƙasar nan damar ganawa da ƴan uwa da abokan arziki.
“Haka kuma kafar na taimakawa wajen haɓaka kasuwanci, samun labarai da sauran bayanan da ake nema.
“Sai dai al’amarin da ya faru a baya-bayan nan dangane da Twitter ya nuna galibin kafafen sada zumunta na bada damar aiwatar da rashin gaskiya, ta hayar yaɗa kalaman karya.
“Haka kuma sun bai wa marasa kishin ƙasa damar, kitsa ayyukan ta’addanci, yaɗa kalaman ƙarya da sauransu” a cewar Buhari.
Shugaba Buhari ya ce waɗannan dalilai ne ya sanya gwamnati taga dacewar dakatar da kamfanin tun a rananr 5 ga Yunin da ya gabata.
Ya kara da cewa biyo bayan dakatar da kamfanin, jami’ansa sunyi ta zarya domin ganin an ɗauke musu takunkumin.
“Bayan zaryar da kamfanin ya yi, ya sanya na kafa kwamitin da zai binciki matsalar tare da kawo dai-dai to”.
“Kwamitin da kuma hukumomin Twitter sun zauna sun kuma tattauna akan muhimman Abubuwa masu yawa, kuma masu muhimmanci”.
You must be logged in to post a comment Login