Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Watanni 18 da suka wuce sune mafi tsauri a zamanin mulki na – Buhari

Published

on

Watanni 18 da suka wuce sune mafi tsauri a zamanin mulki na – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Bauhari ya bayyana cewa watanni 18 da suka gabata sune lokaci mafi tsauri ya fuskanta a zamanin mulkin sa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar a safiyar yau a wani ɓangare na bikin cika shekara 61 da samun ƴancin kai.

Buhari ya ce, Najeriya bata taɓa fuskantar ƙalubale irin wanda ta fuskanta watanni 18 da suka gabata ba.

Har ma ya buga misali da cewa, annobar corona ita ce babbar matsalar da Najeriya ta fsukanata a waɗanann watanni.

Buhari ya tabbatar da cewa, nan ba da jimawa ba zai yi amfani da kujerar sa wajen kawo sauye-sauye masu inganci a ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!