Connect with us

Labarai

Manyan kotunan jihar Kano za su dawo daga hutun da suke

Published

on

Babban jojin jihar Kano, Justice Nura Sagir Umar, ya ce za’a dawo daga hutun da manyan kotunan jihar Kano keyi a ranar Litinin mai zuwa 4 ga watan Oktobar 2021 da muka shiga.

Mai magana da yawun babbar kotun jihar ta Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyan hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radiyo a ranar 30 ga watan Satumbar 2021.

Baba Jibo ya ce manyan alkalan kotunan jihar ta Kano za su ci gaba da gudanar da shar’ar da suke a kotunan su.

A ranar 23 ga watan Augustan shekarar da muke ciki ne dai manyan alkalan kotunan jihar ta Kano suka tafi hutu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!