Labarai
Ɗan jarida tamkar malami yake wajen faɗakarwa – Majalisar malamai
Majalisar malamai ta jihar Kano ya bayyana cewa aikin jarida ya yi kama da aikin malanta ta fannin faɗakarwa.
Shugaban majalisar Malam Ibrahim Khalil ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.
“Ni dai abin da na sani a aikin jarida kamar ko wanne aiki ne akwai daidai akwai kuskure, kuma aikin jarida ya yi kama da aikin malami amma shi ɗan jarida bambamcin sa da malami shi ne gina ɗan adam yadda zai riƙa tunani shi kuma dan jarida zai kawo ma abin da za ka yi tunani a kan sa” in ji Malam Ibrahim.
Malam Ibrahim Khalil ya kuma ce, “Sai ana yin amfani da ƴan jarida wajan haifar da futuntunu, su kuma dama aikin jarida asali ƴan hamayyane suka kafa ta sannan su kuma aikin ƴan jarida kullum sukan fito da abin da zai ɗau hankalin mutane”.
Malamin ya yi zargin cewa akwai kura kurai da ‘yan jarida suke yi wanda su kan su suna kaucewa ƙa’ida.
“Amma futuntuni suna afkuwa ne daga abubuwa daban-daban ba zaka kama Ƴan jarida ɗari bisa ɗari kace sune suke haifar da futuntunu ba, ni dai abin da nasani aikin jarida kamar ko wanne aiki ne akwai daidai akwai kuskure”.
You must be logged in to post a comment Login