Labarai
Ba ni da niyyar takarar shugaban kasa a 2023 – Sanata Ahmed Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa Ya Nisanta Kasansa Da Takarar 2023
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya Allah wadarai da wani rahoto da ya danganta shi da takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2023.
Jaridar Daily Independent ta ranar Jumma’a 17 ga watan July ta fara buga labarin kamin daga bisani Sahara Reporters suka maimaita shi.
A wata sanarwa da mai bashi shawara akan harkar jarida, Ola Awoniyi ya saka ma hannu, Lawan yace abu ne mai sauki a gane cewa irin wannan rahottanin ne ke jama aikin jarida bakin jini saboda karairayi da ke cikin su.
Yace akwai alamun gidajen jaridun sun samo labaran na su ne a hirar gidajen giya don haka yayi kira da ayi watsi dasu.
Yace gaskiya ne shugaban majalisar ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafiin a kira taron kwamitin zartaswa na kasa na jamiyar APC, yana mai kari da cewa irin wannan tattaunawa ba wani sabon abu bane, la’akari da mukamin na Sanata Ahmad Lawan a Najeriya bisa tutar jama’iyar APC.
Sanarwar tace kanzon kurege ne a daganta yunkurin na shugaban majalisar dattawan na hada hannu da shugaban kasa da sauran shuwagabannin jama’iya don warware matsalolin da suka addabi jam’iyar da wani boyayyen shiri na shugaban majalisar.
Ya jaddada cewa abin da ke gaban shugaban majalisar dattawan shine na aiwatar da kudurorin majalisar tarayya ta tara na fuskantar yadda gwamnati zata yi ayyuka don ci gaban yan Najeriya da kuma yadda majalisar zata tallafa ma shugaba Buhari ya cika alkawuran da ya daukar ma yan Najeriya.
Sanarwa tace shugaban majalisar dattawan baya damuwa da irin wannan rahotanin da ake yi don kawo cikas ga aikin da yasa a gaba.
Yace lokaci bai yi ba da za a fara maganar zaben 2023, a maimaikon haka ya kamata a hada karfi da karfe ne domin shawo kan kalubalen dake fuskantar kasar nan ne.
Ya shawarci gurbatattun yan jarida da su nemi wani aikin yi don kauce ma lalata aikin jarida.
Sa Hannu
Ola Awoniyi
Mai ba shugaban majalisar dattawa shawara kan aikin jarida
Asabar, 18th July, 2020
You must be logged in to post a comment Login