Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

15 ga watan Janairu: Bakar rana ga Arewa.

Published

on

Daga Abudullahi Isa

A rana irin ta yau a alif da dari tara da sittin da shida (1966), wasu tsagerun sojoji ‘yan kabilar Igbo, karkashin jagorancin Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogu da Emmanuel Efajuana, su ka kaddamar da wani mafi munin ta’addanci ga al’ummar Arewacin kasar nan. Wadannan sojoji biyu dai sune wadanda su ka jagoranci juyin mulki da ya yi sanadiyar mutuwar Firimiyar Arewa na farko Sir Ahmadu Bello da Firaministan kasar nan Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Masu lura da lamuran yau da kullum dai sun sha nanata cewa, wannan ta’addanci na tsirarun sojojin shi ya yi sanadiyar tsunduma kasar nan cikin halin da ta ke ciki a yanzu, musamman idan aka yi la’akari da irin mutane masu kima da mutunci da ta’addanci ya shafa.

Sauran wadanda wannan ta’addanci na sojojin ya shafa sun hada da: Firimiyar yankin kudu maso yammacin kasar nan Samuel Ladoke Akintola da ministan kudi na lokacin Festus Okotie Eboh da mai dakin Firimiyar Arewa Hajiya Hafsatu Bello da Burgediya Zakari Maimalari da laftanal kanal Abogo Largema da laftanal kanal Kur Muhammed da Kuma laftanal kanal James Pam da dai sauran wasu Mutanen da dama.

Al’umma su dinga kai kara don kwato musu hakki-Majalisar dinkin duniya

Karanta jawabin shugaban kan ranar samun ‘yan cin kai

Asalin kwalejin share fagen shiga jamia ta CAS dake Kano mallakar kabilar Igbo ce

Tun daga wannan lokaci.

Bayanai sun tabbatar da cewa tun daga wannan lokaci zuwa yau, kasar nan ta yi fuskantar matsalolin kwan gaba kwan baya wanda hakan ba ya rasa nasaba da ta’addancin da sojojin su ka yi. Al’ummar Arewa ba  ko shakka za su dade basu manta da mawuyacin halin da su ka shiga ba sakamakon kisan gillar da aka yi ga shugabannin su.

Yanzu dai sama da Shekaru hamsin kenan da aikata wannan ta’addanci, shin kowani darasi alummar Arewa su ka koya daga lokacin zuwa yanzu? Wannan dai tambaya ce da jama’a da dama za su ci gaba da yin ta ganin cewa har yanzu lamura sun kasa kyautatuwa, musamman ganin cewa irin ayyukan alheri da Sardauna ya aiwatar a yankin duk sun zama Tarihi.

Muna Kuma addu’ar Allah ya gafartawa, Sardauna da Tafawa Balewa da sauran wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar wannan ta’addanci da ya faru a ranar goma sha biyar ga watan Janairu.

Rubutu daga Abdullahi Isa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!