Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kai mummunan hari a hanyar Kano zuwa Kaduna

Published

on

An dauki wannan hoton a shekarar 2019 lokacin da direbobi suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja sakamakon kisan wani direba.

Rahotonni daga jihar Kaduna na cewa wasu ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai hari a yankin Fandisho dake mararrabar Jos, kan hanyar Kano zuwa Kaduna.

Shaidun gani da ido sun shaidawa Freedom Radio cewa, da misalin karfe goma na daren jiya Talata ne yan bindigar suka tare hanyar, sa’annan  suka farwa matafiya, inda ake zargin sun yi garkuwa da wasu daga cikin matafiyan, bayan da suka budewa wasu wuta.

Kazalika, mazauna garin sun shaidawa Freedom Radio cewa, maharan sun dauki tsawon lokaci kafin su bar kan hanyar duk da daukin da jami’an tsaro suka kai musu.

Har ila yau, al’ummar garin Kaduna sun wayi gari da ganin zirgar-zirgar motocin bada agajin gaggawa, dana hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa na jigilar wadanda lamarin ya shafa zuwa asibitin sojoji na bataliya ta 44 dake jihar Kaduna.

Wakilin Freedom Radio a Kaduna Haruna Ibrahim Idris yayi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna DSP, Yakubu Sabo kan afkuwar lamarin amma abin yaci tura.

Akwai yiwar sake kai hari a Sakandiren ‘yan mata na Dapchi

Boko haram:sun kai hari kauyukan da kan iyakan jihohin Adamawa da Borno a jiya

Kungiyar boko haram ta kai hari karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa

Kazalika, wakilin namu yayi kokarin jin ta bakin hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa shiyyar Kaduna amma hakonsa bai cimma ruwa ba.

Har ila yau, mazauna garin Mararrabar Jos sun shaidawa Freedom Radio cewa ko a satin da ya gabata, masu garkuwa da mutane sun tsare hanyar inda suka yi garkuwa da mutane kimanin goma sha biyar.

Haka kuma, a makon da ya gabata, wasu gun-gun masu garkuwa da mutane sun afkawa titin zuwa Birnin Gwari ya dangana kauyen Uduwa zuwa  Buruku inda suka yi garkuwa da mutane kimanin sittin ciki har da wani babban malamin Kirista a yankin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!