Labarai
Gwamnan jihar Zamfara ya rantsar da sabbin kwamishinoni
Gwamnan zamfara bello matawalle ya rantsar da kwamishinan ma’aikatar ilimi da kuma ma bashi shawara akan tallafin karatu
A jiya ne Gwamnan jahar Zamfara Alh. Bello Matawallen Maradun ya jagoranci bada rantsuwar aiki ga sabon kwamishinan ilimi na jahar da kuma mai bashi shawara akan tallafin karatu da lamuran Dalibai Dr Ibrahim Abdullahi Gusau da Hon. Luqman B Majidadi.
Rantsuwar wanda babban jojin jahar Mai Shari’a Haji Kulu Ibrahim ta jagoranta ta biyo bayan tantance su da majalisar dokokin jahar tayi.
A jawabinsa, Gwamna Bello Matawalle ya bukace su da suyi aiki tukuru wajen cibiyar da jahar gaba
Hakama Gwamna Matawalle ya shawarci wadanda suka amshi rantsuwar kama aiki da su baiwa mara da kunya wajen ganin an farfado da ilimin jahar Zamfara tare da aiki tare da ma’aikatan ma’aikatarsu.
Dr Abdullahi Gusau wanda tsohon malami ne a jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato, kafin nadin nasa a matsayin kwamishina shine shugaban gudanarwa na shirin IFAD a jahar Zamfara.
Hakama Luqman B. Majidadi wanda ya taba shugabantar kungiyar Dalibai yan asalin jahar Zamfara masu karatu a manyan makarantu daban-daban da ke ciki da wajen Najeriya watau (NUZAMSS) yana rike da mukamin babban mataimaki na musamman ga Gwamna Bello Matawalle.
Rantsuwar ta wadda ta gudana a gidan Gwamnatin jahar Zamfara ta samu halartar mataimakin Gwamna jahar Barr Mahadi Aliyu Gusau, Kakakin majalisar dokokin Rt Hon Nasiru Mu’azu Magarya, Sakatare Gwamnatin jahar Alh. Bala Bello Maru da kwamshinoni da masu Bada shawara da yan siyasa.
Daga Abdullahi Salisu Faru