Connect with us

Labarai

Matawalle ya tabbatar da ‘yan bindaga sun kashe wasu mutane a Zamfara

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara Bello ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 15 sannan kuma suka sace mutane 11 a Jihar.

Bello Matawalle ya tabbatar da hakan ne a jiya yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya jagoranta a fadar gwamnan Jihar da ke Gusau, wanda ya hada da masu rike da sarautun gargajiya da malaman addini da kuma jami’an tsaro.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa ya samu rahoton yadda ‘yan bindigar suka hallaka mutane 13 tare da sace 11 a garuruwan Bingi Nahuche da ke karamar hukumar Bungudu.

Ya kara da cewa ‘Yansakai na Jihar sun yanka wasu Fulani biyu a karamar hukumar Maradun, inda ya umarci kwamishinan ‘yan sandan Jihar da ya gayyaci Sarkin Maradun Alhaji Garba Tambari da kuma Sarkin Arewan Maradun domin yin bayanin dalilin kisan fulanin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!