Labaran Kano
Gwamnatin Kano zata bunkasa tattalin arziki
Gwamanatin jihar Kano ta ce zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta bunkasa tattalin arzikin jihar.
Kwamishinan kasuwanci Alhaji Shehu Na’Allah ne ya bayyana hakan ta bakin babban sakataren ma’aikatar Dakta Lawan Shehu Abdulwahab a yayin karbar bakuncin kungiyoyin dillalan kayayyaki reshen jihar Kano a jiya.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Bashir Habib Yahya ya sanyawa hannu, ta ce, tun a shekarar 2017 gwamnati ta fitar da tsare tsare wadanda za su taimakawa harkokin masana’antu.
Dakta Lawan Shehu Abdulwahab, ya kuma bukaci mambobin kungiyar da su kasance masu bin doka da oda kafin ci gaba da gudanar da tsarin da zai bunkasa kasuwancin su.