Connect with us

Labaran Kano

Gwamantin Kano ta kaddamar da kwamitin bunkasa harkokin noma

Published

on

Gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitin mutane 20 na shirin bunkasa noma da kiwo a jihar.

Shirin dai zai lakume Dala Milyan 95 wanda kuma tallafi ne daga Bankin musulunci dake kasar Saudiyya.

Shirin dai zai mayar da hankali ne kan bunkasa harkokin noma da kiwon dabbobi, da nufin dakile matsalar talauci da kuma samar da wadataccen abinci.

Wannan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a dake kula da shirin Ameen Yassar ya fitar.

Ta cikin sanarwar dai, Mataimakin Gwamnan Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna yayin kaddamar da kwamitin, ya ce,  shakka babu shirin zai taimaka gaya wajen ci gaban daukacin bangaren noma da kiwon dabbobi.

Ya kara da cewa shirin zai bunkasa rayuwar mutane kimanin fiye da milyan daya a daukacin kananan hukumomin jihar 44.

Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar gona Malam Adamu Abdu Faragai, ya ce, shirin zai kuma taimaka wajen magance matsalolin rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da ake samu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,462 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!