Connect with us

Labaran Kano

Kano ba ta bukatar kafa rundunar tsaro -Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, jihar ba ta bukatar kafa wata rundunar tsaro mallakin ta.

Gwamna Ganduje ya bayyana kuma jin dadin sa game da yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikin su a jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar jiya a nan Kano.

Sanarwar ta ce, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da sabon mataimakin Sufeto Janar na yan sanda shiyya ta daya AlG Sadik Abubakar Bello ya kai masa ziyara gidan gwamnati.

A cewar sanarwar, gwamnan na Kano ya nuna gamsuwar sa bisa yadda jami’an tsaro ke gudanar da ayyukan su na tsaron lafiya da dukiyar al’umma, kasancewar wanzuwar hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.

Abdullahi Umar Ganduje ya kara da cewa, shakka babu jihar Kano na amfani da sababbin na’urori na zamani da za su taimaka wajen dakile ayyukan batagari.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,965 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!