Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

2023: ‘Yan Arewa na da ‘yancin tsayawa takarar shugaban kasa a PDP – Gwamnan Bauchi

Published

on

Kwamitin da jam’iyyar PDP ta kafa don nazartar halin da jam’iyyar ta tsinci kanta a zabukan kasa da suka gudana a shekarar 2019, ya bukaci shugaban nin jam’iyyar na kasa da su bar kofar tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar a zaben shekarar 2023 a bude ga kowane bangare na kasar nan.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ne ya bayyana haka lokacin da ya ke mika sakamakon rahoton da kwamitinsa ya tattara kan zabukan da suka gabata, a shalkwatar jam’iyyar da ke Abuja a jiya laraba.

‘‘Mu a binciken da mu ka yi mun gano cewa akwai matsaloli da dama da suka bamu matsala a zabukan da suka gabata, saboda haka sanya batun yanki ko kabila wajen zabukan shekarar 2023 zai janyo mana matukar illa’’

‘‘Akwai masu ra’ayin cewa yankunan kudu maso gabashin kasar nan da kuma arewa maso gabas sune ya kamata a bai wa dama su tsayar da dan takarar shugaban kasa’’

‘‘Sai dai mu a namu ra’ayin wannan ba daidai bane domin Najeriya tana da hakizan mutane daga kowane bangare, saboda haka takaita lamarin akan wani yanki kawai zai cutar da jam’iyyar ce’’ inji Bala Muhammed.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!