Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda cutar amai da fitsarin jini ta mamayi garin Gwangwan da ke Kano

Published

on

Al’ummar garin Gwangwan da ke Kano na cikin fargaba sanadiyyar ɓarkewar cutar amai da fitsarin jini a garin.

Garin na Gwangwan na da nisan kilomita 136 daga birnin Kano, wanda ke yankin ƙaramar hukumar Rogo a ƙarƙashin masarautar Ƙaraye.

A ziyarar da Freedom Radio ta kai garin ta iske yadda al’umma suka yi jungum-jungum cikin alhini sanadiyyar yadda cutar ke mamayar garin.

Alhaji Mai Kuɗi Muhammad Tukur shi ne wakilin garin na Gwangwan ya ce, aƙalla mutane 56 ne suka kamu da cutar, wadda ta ɓulla a unguwanni shida na garin.

Alhaji Mai Kuɗi Muhammad Tukur, wakilin garin Gwangwan.

Yankunan da aka samu ɓullar cutar sun haɗa da unguwar Rijiyar Daɗi da Gwangwan Gabas, da Gwangwan Yamma, sai unguwar Tsarmai da Gangare sai kuma unguwar Ƙofar Fada.

Alhaji Mai Kuɗi ya ce, a rana guda kaɗai sun kai mutane sama da 30 zuwa babban asibitin garin Rogo.

Baya ga waɗanda suka jikkata an kuma sami wani mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar cutar a cewar mai unguwar Gwangwan Ƙofar Kudu Malam Yusuf Tukur.

Mafi yawa waɗanda suka kamu da cutar na koka wa kan yadda cutar ta riƙa laƙume musu kuɗaɗe.

Wani uba Alhaji Shehu Adamu da ƴaƴan sa biyu suka kamu da cutar, ya ce, cikin kwanaki biyu da suka yi a asibiti ya kashe kuɗi har kimanin Naira dubu ashirin.

A gidan Malam Idris Isah Jibrin da muka ziyarta wanda mutane takwas suka kamu da cutar a gidan mun iske su cikin mawuyacin hali.

Wasu daga ciki ko tashi ba sa iya yi, yayin da wasu kuma ba sa iya tsayawa koda sun miƙe sai dai su jingina.

Malam Idris ya ce, shi da matar sa da mahaifiyar sa da sauran ƴan uwan sa suka kamu da cutar.

Ya ci gaba da cewa, a zaman su a babban asibitin garin Rogo zuwa asibitin Gwarzo sun kashe kuɗi har kimanin Naira dubu ɗari biyu.

Freedom Radio ta ziyarci asibitin sha ka-tafi na garin inda muka zanta da Malam Abubakar Rabi’u Ja’afar jami’in da ke lura da asibitin.

Ya ce, cutar ta wuce yadda suke tsammani a don haka ne ya riƙa tura masu cutar zuwa asibitin garin Rogo.

A cewar sa, ya tura mutane sama da talatin zuwa babban asibitin Rogon.

Amma ko da muka ziyarci babban asibitin garin Rogon sai mahukuntan asibitin suka ce, ba su da masaniya kan ɓullar cutar.

Suka ce, mutum ɗaya aka samu ya zo asibitin daga garin na Gwangwan kuma ciwon kansa ya ke fama da shi ba wannan cutar ba.

Garin Gwangwan a karamar hukumar Rogo.

A nan ne muka nemi mu naɗi muryar babban likitan asibitin, sai dai bai amince da hakan ba.

Mun tuntuɓi Malam Sulaiman Ilyasu babban jami’i mai lura da karɓar rahotonnin cutuka a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano.

Malam Sulaiman ya tabbatar da samun rahoton ɓullar cuta a garin, inda ya ce, sun samu rahoton mutane huɗu zuwa biyar, kuma an yi musu gwaji tare da basu kulawa.

Ku kalli wannan rahoto cikin bidiyo:

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!