Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Malami ya rubutawa kwamitin bincikar Magu wasika kan zargin cin hanci

Published

on

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Kasa Abubakar Malami ya rubuta wasika ga kwamitin dake da bincikar dakatacen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Wasikar dai ta bayyanawa shugaban kwamitin Ayo Salami cewa ba zai iya halartar zaman kwamitin ba, sakamakon ayyukan da suke karkashin ofishinsa a halin yanzu.

Wasikar ta Malami na zuwa ne kasa da makwanni biyu da Ministan shari’ar ke ikirarin cewa a shirye yake ya bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.

Sai dai lauyan Dakataccen shugaban hukumar ta EFCC Wahab Shitu ya bukaci kwamitin da ya tilastawa Minsitan shari’ar da ya bayyana gaban kwamitin domin amsa tambayoyin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!