Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun bukaci Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi kan zanga-zanga – NIREC

Published

on

Majalisar kula da addinai ta kasa NIREC karkashin jagorancin mai alfarma sarkin musulmai Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III, da kuma shugaban kungiyar kirstoci ta kasa CAN Dr. Samson Olasupo Ayokunle, sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yiwa ‘yan Najeriya jawabi kan zanga-zangar kawo karshen SARS da ake yi a kasa baki daya.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, biyo bayan samun zanga-zanga a wasu jihohin kasar nan.

Shugabannin ta cikin sanarwar sun bukaci matasan kasar nan da suyi taka-tsan-tsan wajen kaucewa tada fitina, da ka iya kawo rashin zaman lafiya a kasa baki daya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!