Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rikicin kwallon kafa ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi a Kano

Published

on

Wani rikici da ya barke tsakanin wasu matasa a lokacin wasan kwallon kafa ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi a Unguwa Uku.

A ranar Lahadi 11 ga watan Afirilu ne aka buga wani wasan karshe na kwallon kafa tsakanin matasan Unguwa Uku da na Gyadi-Gyadi.

“Lamarin dai ya fusata matasan Gyadi-Gyadin sakamakon rashin nasara a wasan har ya kaiga rasa rai,” in ji shaidun gani da ido.

Bayan an binne matashin da ya rasu ne da safiyar ranar Litinin 12 ga watan na Afririlu, sai matasan Unguwa Uku suka shiga Unguwar Daurawa domin daukar fansa.

Haka zalika, fusatattun matasan da suka tafi daukar fansa sai kuma suka koma yiwa mutane kwacen wayoyi har ma da Babura.

Wakiliyarmu Hadiza Ado Jinta ta rawaito cewa, an yi kokarin tuntubar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar tarho, sai dai bai samu damar amsa wayar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!