Labaran Wasanni
Rashin daukar wasanni a matsayin sana’a shine matsalar Najeriya-Muhammad Abdullahi
Mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta All Star Sheka, ya ce rashin sakawa a rai wasanni sana’a ne da al’ummar kasar nan ba sa yi shine yake kawowa bangaren nakasu.
Muhammad Abdullahi Abubakar da akafi sani da (Dan Malam) ne ya bayyan hakan yayin da yake zantawa da Freedom Radiyo.
Ya kuma ce rashin fitowar ‘yan wasa filin motsa jiki da ake kira da filin atisaye shima na kawowa bangaren koma baya.
All Star Sheka ta doke Ajax Dawakin Kudu a wasan sada zuminci
Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta All Star Sheka wasanni 10 inda yai nasara a wasa 8 yai kuma rashin nasara a wasa 2.
Ya kuma ce babbar matsalar da ake samu a harkokin wasanni a kasar nan shine rashin samun mutanan da za su rinka daukar nauyin kungiyoyin wajen saka kudaden su.
A cewar sa kwallon kafa a yanzu dama baki dayan wasanni sana’a ne da za su iya daukar nauyin kasa.
You must be logged in to post a comment Login