Labarai
Sojoji sun kashe sama da ƴan bindiga 394 cikin mako 3
Shalkwatar tsaro ta ƙasa ta ce sama da ƴan bindiga 394 da ƴan ƙungiyar boko haram 85 ne sojoji suka kashe a wasu manyan ayyuka da suka gudanar cikin mako uku.
A cewar shalkwatar tsaron ta ce an samu nasarar kashe yan bindigar da suka addabi jihohin Borno Zamfara, Kaduna, Kano da kuma Taraba.
Mai magana da yawun rundunar tsaron Brigadier General Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai a Abuja.
Onyeko ya kuma ce, rundunar ta gudanar da ayyuka na musamman tsakanin 2 ga watan Satumba zuwa 30 ga watan.
Ya ƙara da cewa, an kama sama da yan bindiga da yan fashin daji har ma da masu garkuwa da mutane ɗari da biyar, sai kuma sama da 2,783 da suka ajiye makaman su.
You must be logged in to post a comment Login