Labarai
Birki ya ƙwace wa Ganduje – Martanin Ɗansarauniya
Tsohon shugaban Kwamitin jawo iskar Gas zuwa Kano Injiniya Mu’azu Magaji Ɗansarauniya yayi martani ka tsige shi da Gwamna yayi.
A cikin wasu saƙonni da ya shafe daren Litinin yana fitarwa ta shafinsa na Facebook, Mu’azu Magaji ya bayyana cewa birki ya tsinke wa Gwamna Ganduje.
Ya ce, “Dama zaman tare ne da HE AU muke kokarin ceto Jamiyyarmu ta APC…
Tunda Birki ya tsinkewa Baba, yanzu sai mu kauce kada jini ya ɓata mana fararen kayan mu!
Alhamdulillah!
A jira sanarwa kan matsayin mu a siyasa…
Amma dai ba ta tsiya tsiya ba!”
Ɗansarauniya bai tsaya nan ba ya ci gaba da cewa.
“Duk masu yin tafiyarmu ta WIN-WIN Kano Sabuwa amma hancin su a toshe saboda zama tare da mushe a daki daya, to…Alhamdulillah
Allah ya fito damu daga dakin…
Yanzu za mu shaki iskar yanci…
Kuma muyi siyasar yanci da ƙwatowa Kanawa ƴanci”.
Tuni mabiyansa suka shiga tsokaci inda suka riƙa bayyana ra’ayoyinsu a kai.
A nasa ɓangaren abokin tsamarsa a dandalin Facebook ɗan jaridar nan Ja’afar Ja’afar har sabon bidiyo ya fitar a cikin daren inda ya jajanta wa Mu’azu Magaji kan cire shi daga wannan matsayi.
You must be logged in to post a comment Login