Ƙetare
Ana zaman ɗar-ɗar a ƙasar Burkina Faso bayan juyin mulkin da sojoji suka yi tare da tsare tsohon shugaban ƙasar.
Sojojin sun kuma sanya dokar hana fita.
A ranar Litinin ne dakarun sojin ƙasar ta Burkina Faso suka sanar da hamɓarar da Gwamnatin shugaba Roch Kabore, tare da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar da majalisar dokoki.
Sojojin sun sanya dokar hana fita, sannan sun tsare hamɓararren shugaban.
Tun a ranar Lahadin da ta gabata ne aka fara raɗe-raɗin juyin mulkin bayan da aka ji ƙarar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasar.
Sai dai a jiya Litinin ne ya tabbata bayan sanarwar da sojojin suka bayar.
To sai dai duka halin ɗar-ɗar da ake ciki, wasu ƴan ƙasar da ke adawa da hamɓararren shugaban sun take dokar hana fita da sojin suka sanya, inda suka fito kan tituna suna murna tare da nuna goyon baya ga sojojin.
Jam’iyyar MPP ta shugaba Kabore da aka hamɓarar ta bayyana cewa, sojojin na yunƙurin hallaka shugaban da wasu muƙarrabansa.
A nata ɓangaren kuwa ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta yi Al… Wadai da wannan juyin mulki, a wata sanarwa da ta fitar a birnin Abuja.
ECOWAS ta nemi sojojin da su koma bariki, su kuma gaggauta miƙa mulki ga farar hula domin samun daidaito ga matsalolin da ƙasar ke ciki.
Ƙungiya ta ECOWAS ta kuma nemi sojojin da su tabbatar da kare lafiyar shugaba Roch Kabore da suka hamɓarar.
You must be logged in to post a comment Login