Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muhallai sama da miliyan biyu ne suka salwanta a Nijeriya damunar bana: NEMA

Published

on

  • Mutane samada miliyan biyu da dubu dari hudu ne suka rasa muhallansu a Najeriya sakamakom ambaliyar ruwa.
  • An bayyana hakan ne lokacin buɗe taron mako guda na masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Abuja.
  • Taron mako gudan na masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya ya zo dai-dai da lokacin da kasar nan ke farfadowa daga barnar ambaliyar ruwan daya auku.

 

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA Mustapha Ahmed ya ce mutum miliyan biyu da dubu dari hudu ne suka rasa muhallansu sakamakon matsalar ambaliyar ruwan da aka fuskanta a gurare daban-daban a daminar gabata.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne jiya Litinin a Abuja lokacin buɗe taron mako guda na masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya.

Mustapha Ahmed ya ce taron wanda zai horar da jami’an hukumar game da ayyukansu an shirya shi ne a daidai lokacin da kasar nan ke farfadowa daga barnar da ambaliyar ruwar ta haddasa.

Ya kara da cewa mutane 662 ne suka rasa rayukansu, wasu kimanin 3,174 suka samu raunuka, sai kuma miliyan 2, 430, 445 da suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar.

Ranoton: Abdulkadir Yusuf Gwarzo

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!