Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

An Tashi Lafiya

Jami’ar Bayero ta Kano ta karyata jita-jitar Karin kudin makaranta ga dalibai

Published

on

BUK 92 Class

Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero dake Kano ta musanta labarin da ake yadawa na cewa ta kara kudin makaranta ga daliban dake karatu a cikin da wadanda ke Shirin shiga makarantar.
Mai magana da yawun Jami’ar Lamara Garba ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio a daren jiya Litinin.

Lamar Garba ya ce ‘wannan labari da ake yadawa jita-jitar ne kawai wasu ke yadawa, Wanda bashi da tushe.

Ta cikin sakon ya kuma bukaci iyayen dalibai da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulan su,  ‘har yanzu jami’ar bata gama tsayar da matsaya ba kan batun kudin makarantar, dama yadda daliban su biya a bana.

Danna alamar sauti domin domin Jin Karin bayanai.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/01/BUK-KARYA-AN-TASHI-LAFIYA-24-01-2023.mp3?_=1

 

Rahoto: Abdulkadir Yusuf Gwarzo

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!