Labarai
Babbar kotu a Abuja ta umarci DSS ta tahumi Emefiele ko ta sake shi
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/09/Court-Logo.jpg)
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya da ta tuhumi dakataccen Gwamnan Babban Bankin kasa CBN Godwin Emefiele a kotu cikin mako guda ko kuma ta sallame shi.
Kotun ta ba da umarni ne a lokacin sauraron karar da Emefiele ya shigar gaban ta don tabbatar da ‘yancinsa na dan’adam, inda yake kalubalantar kamawa da tsare shi da Hukumar DSS ta yi.
Tun a ranar 10 ga watan Yunin da ya gabata ne Hukumar DSS ta ba da sanarwar cewa ta kama tare da tsare, Godwin Emefiele.
Rahoton: Abdulkadir Yusuf Gwarzo Garzo
You must be logged in to post a comment Login