Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun lalata masana’antar kera bam a Kaduna

Published

on

Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta gano tare da lalata wata masana’antar ƙera makamai a jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X da a baya akafi sani da Twitter, ta ce ta gano masana’antar da ke ƙera bindigogi ba bisa ƙa’ida ba, a garin Kafanchan da ke ƙaramar hukumar Jema’a.

Sojojin sun ce sun shafe mako guda suna tatara bayanan sirri kafin su kai ga gano masana’antar.

Sanarwar ta ce jami’an sojin sun kuma kama mutum guda tare da makamai 22.

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!